Ba na bincikar Jonathan - Buhari

Goodluck Jonathan da Buhari Hakkin mallakar hoto AFP AP
Image caption Shugaba Buhari ya karbi mulki ne a hannun Goodluck Jonathan

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya musanta ikirarin mutumin da ya gada cewa hukomomin kasar na bincikensa kan zargin cin hanci da rashawa.

A ranar Litinin ne Goodluck Jonathan ya ce gwamnatin Mista Buhari ta bincike shi, inda yayi watsi da zargin cewa ya daidaita lalitar gwamnati kafin ya bar mulki.

Sai dai fadar shugaban kasar ta ce zancen na sa hasashe ne kawai, domin babu wata hukuma a kasar da kawo yanzu ke bincikar tsohon shugaban.

"Ba mamaki ya na fargabar cewa binciken da ake yi kan wasu jami'an gwamnatinsa zai kawo ga reshi ne,"in ji mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu.

Mista Shehu ya shaida wa BBC cewa wannan aiki ne na hukumomin bincike, kuma shugaba Buhari ba shi da ikon wanke ko kare wani.

Sai dai ya ki bayyana cewa ko binciken zai iya kaiwa kan Mista Jonathan.

Shugaba Buhari ya zargi tsaffin jami'an gwamnatin da ta shude da satar biliyoyin daloli, kuma da dama daga cikinsu na fuskantar shari'a.

Amma tsohon shugaban ya musanta wannan zargi tare da kare gwamnatinsa a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Bloomberg.

"Mun yi matukar kokari wurin rage cin hanci da rashawa," a cewar Mista Jonathan, wanda ya shugabanci Nigeria daga shekara ta 2010 zuwa 2015.

A watan Mayun 2015 ne Shugaba Buahari ya maye gurbin Mista Jonathan, inda ya zamo shugaba mai ci da ya sha kaye a zabe a karon farko a tarihin Nigeria.