An takura Musulman China kan tafiye-tafiye

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption China ta sanya matakai kan tafiye-tafiye ga Musulmai

'Yan sanda a yankin Xinjiang da ke Arewa maso Yammacin China, sun bukaci a yi wa wasu mazauna yankin gwajin kwayoyin halitta da karbar bayanan haihuwa idan za su nemi izinin yin tafiye-tafiye.

Wannan mataki dai ya shafi Musulman gundumar Yili ne da ke yankin, wadanda aka bukaci su bayar da samfurin jininsu da hoton yatsu da kuma nadar murayarsu a duk lokacin da za su nemi bizar yin wata tafiya.

China ta ce ta dauki wannan mataki ne a kokarinta na dakile hare-haren da take zargin Musulmai masu tsattsauran ra'ayi ke kai wa lokaci-lokaci.

Musulmai da yawa da ke zaune a Xinjiang sun ce hukumomin China suna nuna musu wariya kuma suna yawan hana su damar samun takardu a duk lokacin da suke son yin tafiya.