Dan Japan ya yafe wa iyayensa bayan sun jefar da shi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yamato Tanooka ya yafe wa iyayensa

An sallami wani yaro dan Japan da ya bata har tsawon kwana shida daga asibiti bayan ya bata wani kungurumin daji.

Takayuki Tanooka, mai shekara 44 da matarsa sun bar Tamato Tanooka a bakin hanyar da ke arewacin tsibirin Hokkaido domin su hukunta shi.

Bayan sun dawo sai suka tarar baya nan.

An yi ta neman yaron wanda daga bisani aka gano shi a wani sansanin soji a ranar Juma'ar da ta gabata.

A wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin Mista Tanooka ya ce Yamato ya yafe musu.

Lamarin dai ya jawo muhawara sosai a Japan a kan yadda iyaye ke tarbiyyar 'ya'yansu.