Nigeria za ta tattauna da Avengers

Hakkin mallakar hoto twitter
Image caption Kungiyar Niger Delta Avengers sun dauki alhakin mafiya yawan hare-haren da ake kaiwa yankin

Ministan albarkatun mai na Nigeria, Emmanuel Ibe Kachikwu, ya ce gwamnatin kasar za ta yi tattaunawar sulhu da masu tayar da kayar bayan da ke kai hare-hare kan bututan mai a yankin Naija Delta.

Mista Kachikwu ya ce gwamnati za ta yi hakan ne domin kawo karshen hare-haren da 'yan bindigar ke kai wa da suka yi sanadiyyar raguwar danyan man da kasar ke hakowa.

'Yan kungiyar Niger Delta Avengers ne suka dauki alhakin mafiya yawan hare-haren da ake kaiwa a yankin tun watan Faburairu.

A ranar Talata mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya tattauna da jami'an tsaro da gwamnonin yankin Niger Delta, da nufin kawo karshe hare-haren da kuma samar da kwanciyar hankali a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya Mista Kachikwu na cewa: ''Za a dakatar da duk wani aikin soji a yankin na makonni biyu domin mazauna kauyukan su halarci zaman tattaunawar''.

A cewarsa, gwamnati tana kokarin samar da kwanciyar hankali a yankin inda hare-haren 'yan kungiyar Avengers ke matukar tasiri a kan hakar man

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan kammala taron, gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa, ya ce an yi taron ne saboda bukatar hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi domin gano bakin zaren matsalar.

Man da Najeriya ke samarwa ya ragu zuwa ganga miliyan 1.65 a kowace rana a kan hasashen da aka yi na ganga miliyan 2.2 a kowace rana.

Wannan ya sa kasar na tafka asarar biliyoyin naira a kudaden shigar ta ke samu.