Buhari 'ya saba alkawari' da ya tafi London

Image caption Buhari ya ce ya tafi London ne domin ya huta, sannan ya nemi maganin ciwon kunne

Wani babban likita a Najeriya ya soki shugaba Muhammadu Buhari da saba alkawari bayan da ya tafi Birtaniya domin neman magani.

Ya kamata Mista Buhari ya nuna jagoranci na gari ta hanyar yin amfani da likitoci da kuma asibotocin Nigeria, a cewar Dr Osahon Enabulele, mataimakin shugaban kungiyar likitoci ta kasashen Commonwealth.

Yace 'yan Nigeria sun kashe dala biliyan daya kan neman magani a kasashen waje a shekara ta 2013.

A ranar Litinin ne Mista Buhari ya tashi zuwa London domin neman maganin ciwon kunnen da ya ke fama da shi.

A watan Aprilu ne Shugaba Buhari, a wani jawabi da aka karanta a madadinsa, ya ce ba za a kashe kudaden talakawa ba wurin duba lafiyar jami'an gwamnati a kasashen waje ba, musamman idan wadanda za su iya a Nigeria.

Ya ce ikirarin da jami'an gwamnatin kasar suka yi cewa likitocinsa 'yan Najeriya ne suka ba shi shawarar fita waje domin neman magani ba daidai ba ne.

"Da a ce shugaban kasar ya gayyaci likitocin kasar domin duba shi, da an samu damar inganta fannin kiwon lafiyar kasar," in ji Onabulele, wanda tsohon shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya ne.

A wata sanarwa da ya fitar, Dr Onabulele, ya kara da cewa yawancin manyan 'yan siyasar Nigeria na samun kulawa ne daga likitoci 'yan Nigeria da suke zaune a Birtaniya.

Akwai likitoci 'yan Nigeria sama da 3,000 a Birtaniya, yayin da ake da fiye da 5,000 a Amurka, a cewar Dr Enabule.

Ya kuma zargi gwamnati da kasa wa wurin rage kaurar kwararru daga kasar ta hanyar inganta aiki da kuma asibitocin kasar.