Za a yi sulhu da 'yan Naija Delta — Osinbajo

Image caption Shugaba Buhari ya ce yana so 'yan yankin Niger/Delta su ci moriyar man da ake hakowa a yankin

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce gwamnatinsu tana tattaunawa da shugabanni da al'ummar yankin Naija Delta domin kawo karshen hare-haren da tsagerun yankin ke kai wa kan bututan man fetur.

Wata sanarwa da mai ba shi shawara kan watsa labarai Laolu Akande ya aikewa manema labarai ta ambato Farfesa Osinbajo yana cewa gwamnati ta kara matakan tsaro a yankin domin hana tsagerun ci gaba da kai hare-hare.

A cewarsa, manufar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ita ce duk wani dan yankin ya ci moriyar albarkatun man da ake hakowa daga yankin.

Farfesa Osinbajo ya kara da cewa gwamnatinsu na yin aiki tukuru domin ganin ta rage asarar da take yi sanadiyar hare-haren da tsagerun Naija Delta ke yi kan bututan man fetur din.

Abin da ya sa ba mu fallasa 'barayin' Nigeria ba

Mataimakin shugaban na Najeriya ya ce sun ki bayyana sunayen mutanen da suka sace kudin kasar ne saboda yin hakan zai yi kafar-ungulu a shari'ar da ake yi musu.

Farfesa Osinbajo yana cewa, "Mun fitar da adadin kudi da kadarorin da aka sace, kuma muna sane cewa mutane na tambayar dalilin da ya sa ba mu fadi sunayen barayin ba. Yin hakan zai kawo matsala kan binciken da ake yi a kansu."

A makon jiya ne gwamnatin kasar ta ce ta kwato fiye da Naira biliyan 78 daga hannun wadanda ake zargin su suka wawure kudaden kasar.

A wata sanarwa da ofishin ministan ya fitar, ma'aikatu daban-daban ne suka samu zarafin kwato kudaden daga ranar 29 ga Mayu 2015 zuwa 25 ga Mayu 2016.

Sanarwa ta kara da cewa ana sa ran dawo da kudade daga kasashen ketare da yawansu ya kai dala miliyan 321.

Kazalika, sanarwar ta ce an kwato filaye da gonaki da gidaje da motoci da kuma jiragen ruwa guda 239.