Kwamitin bunƙasa noman shinkafa a Nigeria

Image caption Mista Osinbajo ya ce burinsu shi ne noman shinkafa ya bunkasa nan da shekara daya a Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin na musaman don bunkasa noman shinkafa da alkama a kasar.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo shi ne ya kaddamar da kwamitin karkashin jagorancin gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu .

Mista Osinbajo ya sake jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen ganin kasar ta dogara da kanta musaman a harkar noma shinkafa da kuma alkama.

Ya ce fatan gwamnati shi ne noman shinkafa da alkama ya bunkasa nan da shekara guda.