An mika wa Italiya Madugun fataucin 'yan Afirka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption `yan Afirka da dama sun mutu a hadari kwale-kwale

An tisa-keyar wani dan kasar Eritrea, wanda ake zargi da safarar mutane mai suna Medhanie Mered daga Sudan zuwa kasar Italiya.

Masu shigar da kara a Italiya sun ce Medhanie Mered shi ne Madugun wani gungun masu fataucin mutane da ke yin aika-aikarsu a yankin Afirka ta tsakiya, da Libiya, inda suke kwasar jama'a zuwa Turai.

Galibi sukan yi amfani da jiragen ruwan da lafiya ba ta ishe su ba, suna kuma jibge su da mutane.

A birnin Khartum na kasar Sudan aka tsare Medhanie Mered a wani samamen hadin-gwiwa tsakanin jami'an tsaron Sudan da Burtaniya da kuma Italiya.

A shekara ta 2013 ne aka kaddamar da wannan kawance na jami'an tsaro bayan wani hadarin kwale-kwalen da ya yi sanadin mutuwar masu gudun-hijira sama da 300 a tsibirin Lampedusa na kasar Italiya.