Turkiyya: An cire wa `yan majalisa rigar-kariya

Image caption Shugaba Erdogan na Turkiyya

Shugaban Turkiyya, Recep Tayiip Erdogan ya rattaba hannu a kan wata dokar da ake ce-ce-ku-ce a kanta, wadda za ta cire wa 'yan majalisar dokokin kasar rigar-kariya daga gurfana gaban shara'a.

Magoya bayan jam'iyyar Kurdawa ta HDP na fargabar cewa dokar za ta ba da damar tuhumar duk wani dan majalisar dokokin kasar da ya jibinci 'yan tawayen Kurdawa da laifin aikata ta'addanci.

Gwamnatin kasar a nata bangaren ta ce ya kamata a ce babu dan majalisar dokokin kasar da ya fi karfin doka.