Jirgi marar matuki zai yi aikin tasi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin zai shiga kasuwa nan da karshen shekara

An dai nuna jirgi marar matukin ne a wajen wani baje-kolin kayan laturoni a Las Vegas.

Jirgi marar matukin dai zai iya jigilar fasanja mutum guda ne, kuma shi ne irinsa na farko a Amurka, wanda tuni aka amince a jarraba shi.

Kamfanin Sinawa na EHang shi ne ya kera jirgin, wanda aka rada masa suna 184, kuma kamfanin na fatan cewa zai fara sayar da jirgin a karshen wannan shekarar.

Kawo yanzu dai ba fayyace ba ko za a jarraba jirgi marar matukin ta hanyar sanya masa fasinja.

Kuma babu wani tsari da aka yi ta yanda fasinja zai iya sarrafa jirgin idan aka shiga yanayi na ko-ta-kwana.