An kama mutumin da ke sayar da ƙoda a India

'Yan sanda a Indiya sun ce sun kama wani mutum wanda ake zargi yana sayar da kodar mutune ba a bisa ka'ida ba.

An kama Rajkumar Rao ne ranar Talata a Kolkata, babban birnin jihar Bengalda.

Kwanaki da dama da suka wuce ne dai 'yan sandan kasar suka ce ana yin amfani da wani babban asibiti da ke birnin Delhi mai suna Apollo wajen sayar da koda.

Asibitin Apollo dai ya musanta zargin da ake musu na hannu lamarin.

Wadanda suke wannan kasuwancin, sukan biya wadanda suka sayar da kodarsu dubban daloli, kana su yi musu takardun bogi da ke nuna cewa 'yan uwan marasa lafiyan da ke bukatar koda ne.

'Yan sanda sun ce ana kuma zargin Mista Rao da hannu a wata badakalar a wasu kasashen kudancin Asiya.