Biri ya sa Kenya ta wuni a duhu

Hakkin mallakar hoto KenGen Kenya
Image caption Birin ya janyo Kenya baki daya ta wuni ba wuta

Wani biri ya janyo daukewar wuta a kasar Kenya baki daya bayan ya fada kan wata na'ura mai muhimmanci wajen samar da wutar lantarki ga kasar.

Kamfanin samar da wutar lantarki, KenGen ya ce birin ya fada kan wata transfoma ne a tashar samar da wuta ta Gitaru da ke tsakiyar Kenyar.

Bayan birin ya fada kan tranfomar sai wuta ta dauke dalilin da yasa kasar ta yi asarar ma'aunin wutar lantarki megawatts 180 wanda hakan kuma yasa aka dauke wuta a kasar baki daya.

KenGen ya kuma ce an dawo da wutar bayan tsawon sa'oi hudu kuma birin bai mutu.