Alhinin rasuwar Stephen Keshi

Image caption Stephen Keshi: 1962 zuwa 2016
Mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kan rasuwar tsohon koci kuma kyaftin din Super Eagles ta Nigeria Stephen Keshi, wanda ya rasu yana da shekaru 54.
  • Keshi ya rasu ne sakamakon bugun zuciya
  • Iyalansa sun ce tsohon kocin ya 'huta'
  • Jama'a a sassa daban-daban na nuna alhini
Ku kasance da shafin BBCHausa.com domin samun cikakkun bayanai kan wannan labari da ma sauran labarai daga sassan duniya daban-daban.

12:58 Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Afrika (caf), Issa Hayatou ya ce ya kadu da jin labarin rasuwar tsohon kocin Nigeria Stephen Keshi, wanda ya lashe gasar kofin Africa sau biyu.

Misata Hayatou ya bayyana alhininsa ga iyalin marigayin, yana mai cewa tarihi ba zai manta da shi ganin yadda ya kai kasashe biyu daban-daban zuwa gasar cin kofin duniya - Togo a 2006 da Nigeria a 2014.

Shi ne kocin farko dan asalin Africa da ya jagoranci wata kasa zuwa zagaye na biyu na gasr cin kofin duniya, tare da Nigeria a 2014 a Brazil.

An kuma ta ba zabarsa kocin da ya fi kowanne kwarewa a nahiyar a shekara ta 2013.

Sanarwar ta Mista Hayatou ta kara da cewa Keshi mutum ne da iyalansa da abokansa ke alfahari da shi.

12:45 Ita ma Hukumar kwallon Kafa ta Duniya Fifa ya bayyana alhininta ga me da rasuwar Stephen Keshi:

12:23 Ita ma Sakatare Janar mai jiran-gado ta hukumar kwallon kafar duniya, Fatma Samoura, ta bayyana mutuwar Stephen Keshi da cewa babban rashi ne da fannin kwallon kafa ya yi:

Marigayi Stephen Keshi mutum ne da ba ya nuna kabilanci tsakanin 'yan wasansa, a cewar Rabi'u Ali (Pele) na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Ali Pele, wanda ya buga wasa a karakashin marigayin ya ce "mutum ne wanda ya kware wurin horas wa, amma kuma ba ya son raini. Sai dai ba ya nuna banbancin kabilanci, ko kuma fifita 'yan wasan da ke taka leda a kasashen waje kan na cikin gida".

Hakkin mallakar hoto Getty

Ya kara da cewa mutuwar marigayin ta kada shi sosai, "saboda mutum ne mai hakuri sosai".

Ali Pele ya halarci gasar cin kofin ksashen Africa ta CHAN da Keshi a shekara ta 2014.

11:42 Shugabar Hukumar Tarayyar Afrika Dr Dlamini Zuma ta ce ta kadu da labarin rasuwar Stephen Keshi:

11:22 Keshi tsayayyen mutum ne - Muhammad Annur - BBC Hausa

Marigayi Stephen Keshi mutum ne da ke mai da hankali sosai a kan duk abin da ya sa a gaba, kuma ba ya san raini.

Wasu na ganin saboda yadda yake son nuna iko shi ya sa ma yake da lakabin "The Boss".

Kuma wannan na daya daga cikin dalilan da suka sanya ya samu nasara a lokacin da yake horas da tawagar Super Eagles.

A Nigeria a kan raina kociyoyin gida tare da bayar da fifiko ga 'yan kasashen waje - amma Keshi bai fuskanci wannan matsalar daga wurin 'yan wasansa ba - saboda yana da halin ba-sani-ba-sabo.

Duk da yadda ake ganin mutum ne mai son nuna iko, yana kuma da daukar shawara.

11:20 Kungiyar kwallon kafar Chelsea ta nuna jimaminta kan mutuwar Stephen Keshi:

11:07 Wasu daga cikin fitattun 'yan kwallon Afrika sun bayyana alhinisu game da rasuwar Stephen Keshi, wanda ya rasu ya na da shekaru 54.

Shi ma dan wasan Masar Mido cewa ya yi:

Babban dan wasan Zambia, kuma tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Kalusha Bwalya ya ce:

10:43: Wasu da ke bibiyar shafinmu na Facebook sun bayyana ra'ayoyinsu kan mutuwar Stephen Keshi:

Isma'il Sa'ed: Hakika mutuwar Stephen Keshi babban rashi ne a harkar tamaular Nigeria da ma Afrika baki daya, ganin irin rawar da ya taka a fagen a lokacin rayuwar sa.

Abubakar Musa Qaya: Rayuwa ba ta da tabbas, duniya ba gidan zama ba ce. A gaskiya ba za mu taba mancewa da Keshi ba a fagen kwallon kafar Nigeria saboda gudunmawar da ya bayar.

Rabi'u Nuhu Nabukka: Ina mika sakon ta'aziyya ga iyalan Keshi da 'yan uwansa bisa rashin sa da suka yi. Allah ya ba su hakuri da juriya.

Hakkin mallakar hoto AFP

10:20 Stephen Keshi ne mutum na biyu da ya lashe gasar cin kofin kasashen Afrika a matsayin dan wasa da kuma koci.

Ya na cikin tawagar Super Eagles da ta lashe gasar a Tunisia a shekara ta 1994 bayan ta doke Zambia 2-1 a wasan karshe.

A shekara ta 2013, Keshi ne kocin Nigeria lokacin da ta doke Burkina Faso 1-0 a wasan karshe a Afrika ta Kudu.

Dan kasar Masar Mahmoud el-Gohary shi ne mutumin da ya taba yin irin wannan bajinta.

10:15 Shi ma tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya nuna aihinin rayuwar Keshi:

10:13 'Yan Nigeria su na bayyana alhininsu ga rasuwar tsohon koci kuma kyaftin din kasar Stephen Keshi.

Keshi ya lashe gasar cin kofin Afrika a dan wasa - a 1994 - sannan a matsayin kocin Nigeria a 2013.

Sunday Oliseh ya buga wasa tare da Keshi, kuma ya taba kocin Super Eagles ya ce:

10:01 Jaridar TheCable a Nigeria ta wallafa wata sanarwar da ta ce ta fito daga iyalan Stephen Keshi:

Dan mu, dan uwanmu, kuma sirikinmu, ya riga mu gidan gaskiya inda zai hadu da matarsa da ya su shafe shekaru 35, Mrs Kate Keshi, wacce ta rasu a ranar 9 ga watan Disambar 2015. Keshi ya kasance cikin makoki tun bayan rasuwarta.

Ya yi shirin yin balaguro yau kafin ya gamu da bugun zuciya. Ya samu hutu. Mun gode wa Allah da tsawon ran da ya yi masa. Muna bukatar jama'a su yi la'akari da halin da muka samu kanmu a wannan yanayi mai matukar wahala.

09:51 Wani mai sharhi kan al'amuran wasanni a Nigeria Bolarinwa Olajide ya bayyana alhininsa kan mutuwar Stephen Keshi, yana mai cewa kasar ta rasa jan gwarzo:

09:39 Ba a bayyana abin da ya yi sanadin mutuwarsa ba, amma kafofin watsa labaran Najeriya sun ce Keshi ya mutu ne sakamakon bugun zuciya.

09:29 Da asubahin nan ne hukumar kwallon kafar Najeriya ta bayar da labarin rasuwar Stephen Keshi a shafinta na Twitter.

Hakkin mallakar hoto Getty