Ƙasusuwan mutane 'yan shekara 700,000

kasusuwa Hakkin mallakar hoto Science Library
Image caption A mujallar Nature aka wallafa cikakkun bayanan mutanen

Masana kimiyya sun gano kasusuwan wasu mutane da suka ce sun shafe shekara 700,000 da mutuwa.

Sun kara da cewa kasusuwan na wasu mutan da ne masu kankantar gaske da ake kira 'hobbit'.

An dai yi cikakken bayani a kan wannan halitta a cikin mujallar Nature, inda aka ce kasusuwan da aka gano din na wani mutum guda ne da ya manyanta da wasu yara biyu.

Masana sun kuma ce tsawon mutunen bai wuce mita guda ba.

Mujallar ta ce wadannan kananan mutane sun dade da karewa a doron kasa, tun shekaru 50,000 din da suka shude.