An kai hari kan wani asibiti a birnin Aleppo

Hakkin mallakar hoto AFP

A kalla mutane 15 sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu hare-hare na sama da a ka kai wasu yankunan da ke karkashin ikon 'yan tawaye a birnin Aleppo na Syria.

Kungiyar da ke sa ido da kuma masu fafutika sun ce an kai daya daga cikin harin ne kan wani asibitin tafi-da-gidanka da ke kudancin lardin Shaar.

Hoton bidiyon da aka fitar bayan an kai harin ya nuna gawarwakin da ake fitarwa daga wani gini da aka lalata.

Ba a tabbatar da wanda ya kai harin ba, amma dakarun gwamnati suna kokarin kwace iko da ya rarrabu a hannun 'yan tawaye.