An hari sansanin sojin Ethiopia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Al-Shabab dai ta sha daukar alhakin hare-hare da dama da aka kai Somaliya

Kungiyar al-shaabab ta ce ta kashe fiye da sojojin 40 na Ethiopia a wani hari da suka kai a sansanin kungiyar tarayar Afrika da ke Somaliya.

Sai dai tarayyar ta Afirka ta karyata al-shaabab, tana mai cewa dakarunta ne suka kashe 'yan kungiyar fiye 100.

Mazauna Halgan sun shaida wa BBC cewa sun ji wata kara mai karfin gaske kuma daga bisani suka yi ta bata-kashi.

Kungiyar tarayyar Afirka ta tabbatar da kai harin sai dai ba ta bayyana ko mutum nawa abin ya shafa ba.

Kungiyar dai tana taimakawa gwamanti a yakin da take yi da kungiyar ta Al-Shabab.