An yi taron addu'oi ga Muhammad Ali

Muhammad Ali ya yi fice a duniya

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Muhammad Ali ya yi fice a duniya

Masu ibada da magoya bayan Muhammad Ali na halartar taron addu'o'in da ake yi gwarzon dan damben a birnin Louisville na jihar Kentucky, da ke Amurka.

Ali ne ya tsara zaman addu'o'in na kwanaki biyu shekaru dadama kafin rasuwarsa, kamar yadda mai magana da iyalinsa ya ce.

Imam Zaid Shakir, wanda ya jagoranci taron, ya ce Ali ya nemi a yi masa addu'o'i irin na Musulunci domin su zamo "darasi ga al'umma".

Muhammad Ali, "wanda ake wa lakabi da "The Greatest" "Madugun 'yan dambe", ya rasu ne ranar Juma'ar da ta gabata, ya na da shekaru 74.

Sama da mutane 14,000 ne suka karbi tikitin shiga wurin taron wanda za a yi a Louisville, inda Ali ya gwabza damben sa na karshe a 1961.

Al'umar Musulman Amurka da ke halartar addu'o'in sun ce suna fatan taron zai zamo wata dama ga Amerikawa su kare fahimtar addinin Musulunci da kuma aikace-aikacensa.

A shekarar 1964, Ali ya karbi addinin Musulunci, sannan ya sauya sunansa daga Cassius Clay, wanda ya ce sunan sa ne "bauta".