Kamfanonin jiragen sama za su janye daga Nigeria

Jirgin saman Iberia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jirgin saman Iberia

Masana harkar zirga-zirgar jirage sama a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu game da janyewar da wasu kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suke cewa za su yi sakamakon matsatsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi.

A watan da ya gabata kamfanonin jiragen sama na Iberia na kasar Spain da United Airlines na Amurka suka sanar da dakatar da zirga zirgar jiragensu na yau da kullum a Najeriyar.

Kamfanonin sun ce rashin kasuwa da kuma sarkakiyar da ke tattare da samun kudaden kasasen waje suka tilasta musu daukar wannan mataki.