'Babu alaƙa tsakanin Boko Haram da IS'

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Boko Haram ta yi mubaya'a ga IS fiye da shekara daya da ta wuce

Wasu jami'an gwamnatin Amurka sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa babu wata hujja da ta nuna cewa 'yan Boko Haram sun samu taimakon kudi ko kayan aikin daga kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci.

Jami'an sun bayyana haka ne a daidai lokacin da mayakan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari a garin Bosso na Jamhuriyar Nijar, wanda ke kan iyaka da Najeria, inda suka kashe sojoji 26.

Reuters ya ambato 'yan Boko Haram na cewa sun kai harin ne a matsayinsu na 'yan kungiyar IS da ke yammacin Afirka.

Fiye da shekara daya kenan tunda shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau, ya ce sun yi mubaya'a ga IS.

Jami'an gwamnatin ta Amurka da dama, wadanda ba sa so a bayyana sunayensu, sun shaida wa Reuters cewa Boko Haram ta yi mubaya'a ga IS ne domin kawai ta kara yin suna a idanun duniya, sannan ta ja hankalin wadanda za su so shiga cikinta da kuma samun tallafin kudi.