Zaben Peru: Pedro Pablo shi ne a gaba

Pedro Pablo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Pedro Pablo

Tsohon ma'aikacin bankin duniya,Pedro Pablo Kuczynski shi ne ya lashe zaben shugaban kasa na kasar Peru a fafatawar mai zafi da aka yi a cikin shekarun da suka gabata.

Ya yinda har yanzu akwai kashi daya bisa uku na kuri'un da ba a kirga ba amma hukumomin zabe sun bayana cewa ya samu kashi hamsin da daya cikin dari na kuri'un da aka kirga

Ita kuwa abokiyar hammayarsa Keiko Fujimori wadda ita ce diyyar tsohon shugaban kasar da ke tsare a gidan yari Alberto Fujimoi ta samu kashi arbain da tara na kuri'un

A jawabin da ya yiwa magoya bayansa Mista Kuczynski ya ce yana son ya hada kan alummar kasar .

Sai dai har yanzu Madam Keiko ba ta amince da shan kaye ba.