Ramadan ya zo - tumatir ya sauko

Masu sayar da tumatir
Image caption Manoma sun tafka mummunar asara sakamakon tsutsur tumatir

Yayin da farashin kayayyakin masarufi ke kara tsada a Nigeria, da alama sauki ya dan fara samuwa bayan da farashin tumatir, wanda ake bukata domin amfanin yau da kullum wajen girki, ya fara faduwa da kusan kashi daya cikin uku idan aka kwatanta da yan makonnin da suka wuce.

Makonni kadan da suka wuce, layin 'yan tumatir na kasuwar 'yan Kaba a birnin Kano kamar an yi shara, domin babu komai sai masu sayar da tumatur din kawai suna zaman jiran kota-kwana.

Wannan ya faru ne sakamakon annobar tsutsa ta afkawa gonakin tumatir a wasu jihohin arewa, abinda ya sa farashinsa yin tashin gwauron zabi da kuma karanci matuka.

Sai dai yanzu al'amura sun fara farfadowa a kasuwar domin kuwa tumatir din ya fara samuwa, kuma wannan abin farin ciki ne ba wai kawai ga 'yanh kasuwar ba, har ma da jama'ar gari, musamman ganin yadda aka shigaa watan azumi.

A yanzu farashin kwandon tumatir kan kama daga Naira dubu tara zuwa Naira dubu 12, maimakon Naira dubu 35 zuwa dubu 40 a baya-bayan nan.

'Tsugune ba ta kare ba'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Amma fa a iya cewa tsugune ba ta kare ba kan matsalar karancin tumatur a gonakin jihar Kano.

Domin kuwa a cewar 'yan kasuwar har yanzu tsutsar ta tumatur ba ta bar gonakin jihar ba, don haka suna saro tumaturin ne daga makwabtan jihohi.

'Yan kasuwar kan niki gari ne zuwa garuruwan da ke jihohin Kaduna da Filato domin safarar wannan kayan gwari zuwa Kano.

Shugaban kungiyar 'yan kasuwar tumatur a 'yan kaba, Malam Nuhu Yaro, ya ce ''sabanin Kanon, cutar Ebola ta tumatur wadda ta haddasa dumbin asara ga manoma, ta yi sauki a wasu gonaki na makwabtan jihohin Kano".

''Don haka ne muke zuwa can domin sayowa don dai a samu wadatarsa da kuma saukinsa, maimakon dogara da kadan din da ake samu a gonakin garuruwan jihar Kano,'' in ji Malam Nuhu.

'Kaka-ni-ka yi'

Image caption Jama'a da dama ba sa iya sayen tumatir saboda tsadar da ya yi

Sai dai wani abu da ke ci wa masu sayar da tumaturin tuwo a kwarya shi ne yadda ganin cewa ga tumaturin ya fara samuwa amma kuma rashin walwalar aljihu yasa mutane ba sa zuwa saya.

'Yan kasuwar da dama sun shaida wa BBC cewa a kan dole suke karyar da farashin tumaturin su ci karamar riba musamman idan rana ta take.

Wani dan kasuwar ya ce, ''Idan ma bamu karyar da farashinsa ba to a karshe kwantai za mu yi kuma zai iya lalacewa.''

Wasu daga cikin masu sayen tumatir din sun ce wahalar rayuwa ta sa su kan hakura da tumatir din a wasu lokutan.

Image caption Har yanzu tsutsar tumatir din ba ta kauce gaba daya ba

''Wani lokaci ala dole muke saya don bukatarsa amma wani lokacin a dole mu ke hakura ko muna so saboda rashin kudi duk da cewa farashinsa ya sauko,'' a cewar wani magidanci.

A yanzu haka dai a iya cewa tun lokacin da gwamnatin tarayya ta ce ta samo maganin tsutsar tumatur mai suna Tuta Absoluta, manoman kasar suka fara farin ciki da tsammanin samun tallafi daga gwamnati.

Suna kuma sa ran nan ba da jimawa ba za su mayar da asarar biliyoyin nairar da suka tafka na lalacewar amfaninsu.