Wasiyyar Muhammad Ali

Muhammad Ali Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane 14,000 ne suka halarci addu'o'in Musulunci da aka yi wa marigayin

Fitaccen dan damben duniya Muhammad Ali, wanda ya rasu yana da shekaru 74, ya bar wasiyya kan wasu al'amura da suka shafe shi, musamman yadda za a binne shi idan ya koma ga Allah.

Babban abin da ya fi fice daga cikin wasiyyar Muhammad Ali shi ne yadda ya tsara irin yadda yake son jana'izarsa ta kasance.

Marigayin ya bayyana cewa yana so a kare masa akidarsa ta addinin Musulunci, inda ya nemi iyalansa da su tabbata cewa an binne shi a tsari irin na Islama.

Mai magana da yawun iyalinsa ya ce Ali ne da kanshi ya tsara zaman addu'oi na kwanaki biyu da za a yi masa shekaru da dama kafin rasuwarsa.

Sannan ya nemi da a tabbatar da cewa duk wanda ya kamata ya halarci jana'izar ya halatta, domin acewarsa shi mutum ne na mutane.

Imam Zaid Shakir, wanda ya jagoranci taron addu'ar da aka yi a ranar Alhamis, ya ce Ali ya nemi a yi masa addu'o'i irin na musulunci a lokacin jana'izarshi domin su zamo "darasi da al'umma".

Ga yadda jana'izar za ta gudana:

A shekarar 1964 ne dai zakaran damben duniyan ya Musulunta, kuma ya sauya sunansa daga Cassius Clay, abinda ya kira sunan "bayi".

An dai fara jana'izar ne a ranar Alhamis, inda mutane 14,000 suka halarta, yayin da ake sa ran 18,000 za su halarci na ranar Juma'a.