'Yan gudun hijira na karuwanci a Girka

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Daruruwan 'yan gudun hijira ne ke son shiga Turai duk shekara

Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano kananan yara 'yan gudun hijira na karuwanci a Athens, babban birnin Girka.

Akasarinsu su na so su shiga arewacin Turai amma sabbin ka'idojin kan iyaka ya sa sun makale kuma ba su da wata halastacciyar hanyar da za su nemi kudi.

Azat, matashi ne dan kasar Iran mai shekara 25, ya kuma bayyana nadamarsa a kan mu'amala tsakaninsa da maza wadanda su ka girme shi inda suke bashi dala 5 ko 10.

BBC ta ga yara da dama a wurin shakatawa na Athens su na jira a dauke su.

Wani yaro dan kasar Afghanistan da ke wannnan sana'a ya ce yara maza wadanda shekarunsu bai wuce 15 ba na tallan kansu domin su samu kudi.