Tsohon kocin Nigeria Amodu Shu'aibu ya rasu

Image caption Amodu Shu'aibu ya rike Super Eagles karo hudu

Allah ya yiwa tsohon kocin kungiyar kwalon kafa ta Najeriya, Super Eagles, Amodu Shu'aibu rasuwa, yana mai shekaru 58.

Marigayin, wanda shi ne daraktan kwalon kafa a Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya (NFF), ya rasu ne a safiyar ranar Asabar, kamar yadda NFF ya bayyana.

Sakataren Hukumar ta NFF, Dr. Muhammad Sunusi ya shaida wa BBC cewa Amodu Shu'aibu ya rasu ne bayan ya koka da ciwon kirji, a daren ranar Juma'a.

Kafin rasuwarsa, marigayi Amodu, ya rike kungiyar Super Eagles har karo hudu, a matsayin koci.

Dr Sanusi ya kara da cewa a yammacin ranar Asabar ne za a yi jana'izar marigayin, a mahaifarsa da ke jihar Edo a Kudu maso Kudancin Najeriya.

Mutuwar tsohon kocin na zuwa ne kwanaki uku bayan rasuwar kaftin kuma tsohon kociyan Super Eagles, Stephen Keshi.

Amodu da Keshi sun yi aiki tare a matsayin babban koci da kuma mataimaki, a lokacin gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2002, da aka yi a kasar Mali.