Wane ne Amodu Shu'aibu?

Asalin hoton, AFP
Amodu Shu'aibu ya taka rawar gani sosai a Najeriya
Mutane da dama musamman wadanda suka san marigayi, tsohon kocin kungiyar wasan Najeriya, Amadu Shu'aibu.
Ga wasu daga cikin ra'ayoyin da Nura Muhammad Ringim ya tattaro mana daga Kaduna.
Jama'a da dama ne suka halarci jana'izar tsohon kocin Super Eagles ta Najeriya, Amodu Shu'aibu, wanda ya rasu a daren Juma'a yana da shekaru 58.
An binne marigayin ne a mahaifarsa da ke garin Okpella na jihar Edo, a Kudancin Najeriya, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sakataren Hukumar kwallon kafa ta kasar (NFF), Dr Muhammad Sunusi, ya shaida wa BBC cewa marigayin ya rasu ne bayan ya koka cewa yana fama da ciwon kirji.
A sakon ta'aziyyar da ya aike a shafinsa na Twitter, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya kadu da mutuwar, yana mai adu'ar Allah ya jikan marigayin.
Mutuwar ta Daraktan kwallon kafa na hukumar ta NFF ta zo ne kwanaki kadan bayan rasuwar tsohon koci kuma kyaftin, Stephen Keshi, wanda ya mutu yana da shekaru 54.
Shugaban Hukumar NFF Amaju Pinnick ya ce: "Wannan wani bala'i ne da ya kara samun mu. Har yanzu muna jimamin Keshi, kuma sai ga Amodu ya tafi."
Asalin hoton, Getty
Amodu ya rike Super Eagles har karo hudu.
Amodu ya fara jagorantar Najeriya tun yana dan shekara 36 a shekara ta 1994.
Marigayin ya samarwa Super Eagles gurbin shiga gasar cin kofin duniya a 2002 da 2010, sai dai bai jagoranci tawagar zuwa gasar ba.
A lokacin sa ne Najeriya ta kare a mataki na uku a gasar cin kofin kasashen Afrika a Mali a shekara ta 2002 da Angola a 2010.