Za a kawo 'karshen' kisan mutane a Bangaldesh

Sheikh Hasina Hakkin mallakar hoto focus bangla
Image caption Sheikh Hasina na fuskantar matsin lamba daga 'yan adawa

Fira Ministan kasar Bangladesh, Sheikh Hasina, ta ce gwamnatinta za ta yi iya bakin kokarinta wajen kawo karshen kashe-kashen da ake fama da su a kasar.

A 'yan kwanakin nan ana yawan kashe mutane marasa rinjaye da kuma marubuta wadanda addini bai dame su ba a sassan kasar daban-daban.

Ana dai dora alhakin kisan kan masu kaifin kishin Islama.

Wannan bayani nata yazo ne kwana guda bayan 'yan sanda sun kaddamar da aikin fatattakar masu tsattsauran ra'ayin addini.

Mahukunta a kasar sun ce an kama mutane fiye da 1,000 tun bayan da aka fara aikin a tsakar daren ranar Alhamis din da ta gabata.

Jam'iyyar adawa a kasar ta Nationalist Party ta ce gwamnati na amfani da wannan aikin na kama ba-ta-garin ne domin kama 'yan adawarta na siyasa.