Hargitsin 'yan wasan kwallo a Faransa

Hakkin mallakar hoto AP

An samu hargitsi tsakanin magoya bayan kungiyoyin wasa na Ingila da Rasha, a gasar wasan Euro 2016 da aka yi a birnin Marseille na kasar Faransa.

Yan kasar Birtaniya da dama ne dai ke kwance a asibiti a kasar Faransar sakamakon arangamar.

Kafin fara wasan dai, 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla da ruwan zafi domin tarwatsa masu arangamar da juna a dab da filin wasa.

Shaidu sun ce hargitsin ya fara ne a filin wasan bayan da aka yi kunnnen doki tsakanin yan wasan Ingila da Rasha, inda bayan kammala wasan magoya bayan Rasha suka fara kai wa na Ingila hari a cikin filin wasa.

Yansandan kwantar da tarzoma a birnin na Markseille, sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla kan daruruwan magoyan bayan kungiyoyin wasan kwallon kafar na kasashen Birtaniya da Rasaha da Faransar don tarwatsa su.

An kuma yi ta jifa da kujeru da kwalabe a arangamar kan titinan.