An yi jana'izar Muhammad Ali

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane suna kai gaisuwa ga gawar Muhammad Ali, yayin da ake wucewa da ita.

Kimanin mutane dubu 14 ne suka halarci taron nuna alhini da jana'izar, shahararren dan damben nan Muhammad Ali.

An dai gudanar da jan'izar ne a Luisville da ke jihar Kentucky ta Amurka.

Taron ya samu halartar mutane daga bangarori addini da rayuwa daban-daban.

Musulmai da Kiristoci da ma Yahudawa duka Mutane da dama sun yi bayanai masu gamsarwa kan nasarorin da marigayin ya samu a fagen wasanni da zamantakewa da ma siyasa.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fitaccen jarumin fina-finan Amurka, Arnold Schwarzenegger, a wurin jana'izar Ali

Shugaban Amurka, Barack Obama ya yabi Muhammad Ali, a wani sako da ya aike da shi.

Shi ma tsohon shugaban Amurkar, Bill Clinton ya bayyana Ali da mutum mai imani wanda ya san cewa Allah ne yake da iko da shi.

Fitaccen jarumin fina-finan Amurka, Will Smith da zakarun dambe, Mike Tyson tare da Lennox Lewis ne suka dauki makarar da marigayin ke ciki, a lokacin da za a binne shi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Will Smith da sauran zakarun dambe

Kafin nan dai sai da Hamza Abdul-Malik, ya bude taron da karatun Al'kur'ani mai girma.