Omar Mateen ne ya harbe 'yan luwadi 50 — FBI

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Obama ya yi Allawadai da harin

Hukumar binciken laifuka ta Amurka, FBI ta ce ta gano mutumin da ya kai harin bindiga a wurin shakatawar masu luwadi, a inda kuma ya kashe mutane 50.

Hukumar ta ce sunan mutumin Omar Mateen kuma dan Amurka ne.

FBI ta ce kafin bude wutar, sai da Omar ya yi mubaya'a ga kungiyar IS, ta hanyar kiran layin neman agajin gaggawa na Amurka wato 9-1-1.

Tuni dai shugaban Amurka, Barack Obama, ya bayyana harin da aka kai kan matattarar masu luwadin, da harin ta'addanci da nuna kin jinin wata al'umma.

Sai dai kuma Obama ya yi gargadin cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda bindiga ta zama gidan kowa akwai.

Shi kuwa dan takarar shugabancin Amurkar, karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump ya soki Obama ne da Hillary Clinton kan cewa sun ki fitowa fili su bayyana wa mutane cewa hari ne da 'yan ta'addar Musulmi suka kai.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jami'an tsaro sun kai agajin gaggawa

Magajin garin Orlando da ke Florida ta Amurka, ne dai ya bayar da sanarwar cewa mutane 50 ne suka mutu sakamakon harin.

Wannan dai shi ne harin bindiga mafi muni da aka taba kai wa Amurka a tarihin kasar a shekarun baya-bayan nan.

Wasu mutane 53 din kuma sun jikkata, suna kuma karbar taimakon gaggawa a asibiti.

Kafofin yada labaran Amurka sun gano mutumin da ya bude wutar a matsayin dan Amurka mai suna Omar Mateen.

Matashin mai shekara 29 yana dauke ne da babbar bindiga da kuma karama ta hannu a lokacin da ya bude wutar.

Ya yi garkuwa da mutane kusan 30 kafin daga bisani 'yan sanda suka harbeshi har lahira.