An kai hari kan 'yan luwadi a Florida

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jami'an tsaro sun je wajen domin ceto

'Yan sanda a Amurka sun ce mutane da dama ne suka jikkata yayin da wani ya bude wuta a mashayar da masu auren jinsi daya ke taruwa a birnin Florida na Orlando.

'Yan sandan Orlando sun fada a shafin Twitter cewa tuni dan bindigar da ya bude wutar a mashayar ta Pulse da ke tsakiyar birnin ya mutu.

Tuni jami'an tsaron da suka kware wajen kwance bam suka je wajen, kuma an samu fitar da wani bam da bai kai ga fashewa ba.

'Yan uwa da dangin wadanda abin ya shafa sun taru a asibitoci inda suke cikin tashin hankali kan fargabar rasa 'yan uwansu.

'Ganau'
Hakkin mallakar hoto epa

Wata mata ta ce 'yarta ta aika mata sakon kar ta kwana da kuma ta kirata a waya daga mashayar inda ta shaida mata cewa an harbeta a kafada.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce sun ji a kalla harbin bindiga sau 20.

Fiye da mutane 100 ne suke cikin mashayar, wadda aka santa a matsayin wadda ta fi kowacce tashe a birnin.

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa, dan bindigar ya bude wutar ne da misalin karfe na tsakar daren Amurka.