Za a dawo da 'yan hijirar Nigeria daga Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan gudun hijirar Najeriya ke samun mafaka a Kamaru

Najeriya ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, da kuma jamhuriyar Kamaru, kan mayar da wasu 'yan gudun hijirarta cikin aminci da suke samun mafaka a Kamaru.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, Muhammad Sani Sidi ne ya bayyana hakan yayin da wata tawaga ta kungiyar Tarayyar Afrika karkashin jagorancn kwamishinar harkokin siyasa ta kungiyar Dakta Aisha Laraba Abdullahi, ta kai musu ziyara.

Ya ce akwai kusan 'yan gudun hijirar Najeriya dubu 80 da yanzu haka suke samun mafaka a Kamaru, kuma gwamnati na iya bakin kokarinta domin ganin ta biya musu muhimman bukatunsu.

Sidi ya kara da cewa gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin da al'amarin ya shafa da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da masu zaman kansu sun yi matukar kokari cikin shekara hudu da ta gabata wajen tallafawa 'yan gudun hijira a yankin area maso gabashin Najeriya.

''Yanzu mun kammala da aikin bayar da agajin gaggawa zuwa na farfadowa da mayar da 'yan gudun hijira muhallansu,'' in ji Sidi.

NEMA ta kuma yi kira ga Tarayyar Afrika da ta kara hobbasa wajen ganin ta taimakawa wadannan 'yan gudun hijira.

Tun da fari dai tawagar Tarayyar Afrikan ta ce ta zo Najeriya ne domin ganbewa idonta halin da 'yan gudun hijirar ke ciki, sakamakon rahoto da take da shi cewa akwai 'yan gudun hijira kusan miliyan 13 a nahiyar.