An kashe tsaffin jami'an Gaddafi 12

Fursunoni a Libya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Babu cikakken bayani kan yadda aka kashe mutanen

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Libya, Martin Kobler, ya yi Allah-wadai da kisan wasu fursunoni 12 bayan an sallame su daga gidan yari.

An gano gawarwakin mutanen ne a sassan birnin Tripoli daban-daban, kwana guda bayan sakin nasu.

An tuhume su da hannu wurin kashe wa da kuma muzguna wa masu zanga-zangar da ke adawa da tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a 2011.

Sai dai wata kotu ta sallame su tare da sanya musu wasu sharudda.

Ofishin mai gabatar da kara ya ce an harbe mutanen ne dukkansu. Amma babu cikakken bayanin yadda aka kashe su.

Jami'ai sun ce mutanen sun bar gidan yarin ne tare da 'yan uwansu a ranar Alhamis, sai dai babu tabbas kan wannan ikirari.

Hadin gwiwar 'yan bindiga da kuma 'yan sandan bangaren shari'a ne ke kula da mafi yawan gidajen yari a Libya.