Microsoft zai sayi shafin LinkedIn

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shafin LinkedIn yana da miliyoyin mabiya a duniya

Kamfanin Microsoft ya bayar da sanarwar sayen shafin sada zumunta na LinkedIn, kan dala biliyan 26.

Wannan dai shi ne ciniki mafi girma da Microsoft ya taba yi.

Ana ganin sayen shafin na LinkedIn zai taimaka wa Microsoft bunkasa sayar da manhajojinsa na kasuwanci da kuma tura sakonnin e-mail.

LinkedIn yana da sama da mutane miliyan 430 da ke amfani da shafinsa a duk fadin duniya.