Ana shirin yanke wa Pistorius hukunci

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Da farko dai an yankewa Oscar hukuncin sheka biyar a gidan yari

An fara zaman sauraren bahasi kan hukuncin da za a yanke wa dan tseren kasar Afrika ta Kudu Oscar Pistorius wanda ya kashe budurwarsa, Reeva Steenkamp, a Pretoria.

Ya na fuskantar daurin a kalla shekara 15 a gidan kaso amma kuma za a iya rage masa yawan shekarun sakamakon lokacin da ya riga ya shafe a gidan yarin da ma kuma wasu dalilan.

Ana sa ran za a kwashe mako guda ana sauraron karar inda za a yanke hukunci a ranar Juma'a.

Pistorius, mai shekara 29, ya kashe Ms Steenkamp ne a watan Faburairun shekarar 2013 bayan ya yi harbi sau hudu a kofar bandakin da ke a rufe.

Dan wasan dai ya dage a kan cewa ya yi harbin ne domin farma wani baro da ya shiga gidansa a lokacin.

Da farko dai an yanke masa hukuncin shekara biyar a gidan yari a kan kisa ba dagangan ba, amma a watan Disamba ne aka sauya hukuncin zuwa kisa da gan-gan bayan masu shigar da kara sun bukaci hakan.