NDA ta sanya sharuddan sasantawa da gwamnati

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu tayar da kayar baya na kai hare-hare kan bututan man

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta Niger Delta Avengers (NDA), a Nigeria, ta ce a shirye take ta hau teburin tattaunawa da gwamnatin kasar domin kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu.

Amma kuma ta ce za ta yi hakan ne idan gwamnatin ta bi sharuddan da ta fitar a ranar Talata.

A wata sanarwa da ta fito daga hannun kungiyar, ta ce tana so kamfanonin man fetur na kasashen waje da suke aiki a Najeriya su kawo masu sulhu daga kasashensu, "idan har ana so a samu zaman lafiya mai dorewa".

Ta kara da cewa bata amince gwamnatin Najeriya ta gabatar da masu sasantawa daga bangarenta ba domin ba ta yarda da su ba.

Sanarwar ta ce, ''Idan kuma ba a yi mana yadda muke so ba, to akwai yiwuwar mu sauya maganarmu ta farko ta cewa ba za mu kashe kowa ba.''

''Za mu ci gaba da yin duk wasu abubuwa da muke yi tare da kara kaimi wajen yin su, idan har gwamanati da kamfanonin mai basu cika wadannan sharudda ba, da yin gyare-gyaren da suka dace da kuma dakatar da sayen danyen mai daga yankinmu,'' a cewar sanarwar.

Hakkin mallakar hoto Abduallhi Kaura
Image caption Gurbatar muhalli a yankin Niger Delta

Kungiyar ta NDA ta ce tana wannan fafutuka ne domin kwato 'yancin yankin, wanda ke fuskantar matsanancin talauci da gurbatar muhalli sakamakon malalar mai, don ganin sun ci moriyar albarkar da ke yankin.

Tun a farkon shekarar nan kungiyar ke kai hare-hare kan bututan mai, wadanda suke yin matukar tasiri ga tattalin arzikin Najeriya, har ma suka shafi raguwar man da kasar ke samarwa.