An dakatar da jam'iyyar Shi'a a Bahrain

Bahrain Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Shi'a sun dade suna zanga-zanga a Bahrain

Kasar Bahrain ta dakatar da jam'iyyar 'yan Shi'a masu adawa a wani mataki da ake wa kallon na muzgunawa masu hamayya da gwamnati ne.

Ma'aikatar Shari'a ta kasar ta ce an kuma toshe asusun banki da kadarorin jam'iyyar Al-Wefaq.

Al-Wefaq ita ce jam'iyya mafi girma ta 'yan Shi'a, wadanda ke da rinjaye a kasar.

Suna zargin cewa mahukunta na muzguna musu da kuma nuna musu banbanci.

A yanzu haka shugaban jam'iyyar Sheikh Ali Salman, yana tsare a gidan yari.

An kara tsawon hukuncin da aka yanke masa daga daurin shekara hudu zuwa tara.

Ranar Litinin ne kuma mahukunta suka sake tsare wani mai fafutuka Nabeel Rajab.

Mabiya Shi'a sun ci gaba da zanga-zanga jefi-jefi tun bayan da jami'an tsaro suka kawo karshen boren da aka yi a 2011.