Buhari ya yi tur da kisan 'yan luwadi a Amurka

Omar Mateen ya dade yana zuwa gidan rawar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Omar Mateen ya dade yana zuwa gidan rawar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da wani mutum mai suna Omar Mateen ya kai a gidan rawar da 'yan luwadi ke yin sharholiya a birnin Orlando na Amurka.

Akalla 'yan luwadi da madugo 49 ne aka kashe a harin, yayin da wasu 53 suka jikkata.

Wata sanarwa da kakakin Mista Buhari Femi Adesina ya fitar, ya ce abin da Omar Mateen ya aikata "laifi ne da matsorata" ke aikatawa.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin Najeriya ta aike wa Amurka wasika ta hannun jakadanta James Entwistle, inda ta bayyana alhininta ga Shugaba Barack Obama da al'umar Amnurka kan abin da ya faru.

Shugaba Buhari ya jaddada aniyar Najeriya ta ci gaba da bayar da goyon baya a kan yaki da 'yan ta'adda.

Ya kuma yi kira ga kasashen da ke son zaman lafiya da su zage-dantse wajen kawar da masu tsattsauran ra'ayi a doron-kasa.

'Ya samu tsaurin ra'ayi a Amurka'

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Jama'a da dama sun nuna alhininsu kan harin

Rahotanni daga Amuka sun ce Omar Mateen ya daɗe yana kai ziyara gidan sharholiyar 'yan luwadin.

Jaridun ƙasar sun ambato wasu da ke mu'amala da gidan rawar na Pulse da ke Orlando na cewa sau dama suna ganin sa a wajen yana shan wani abu, wasu lokuta kusan sau 12

Shugaba Obama ya bayyana cewa Omar ya kai harin ne sakamakon tsaurin ra'ayin addinin da ya samu a cikin Amurka.

Shugaban na Amurka ya ce zai je jihar Florida ranar Alhamis domin ya jajantawa iyalan mutanen da Omar Mateen ya harbe.

Shi kuwa dan takarar neman shugabancin Amurkar, na jam'iyyar Republican, Donald Trump ya bayyana tsarin shige da ficen Amurka a matsayin mai rauni tun da har aka bar iyalan Omar Mateen suka shiga kasar daga Afghanistan.

Sai dai Hillary Clinton, wadda za ta yi wa jam'iyyar Democrat takarar shugabancin kasar, ta ce za ta kawo sauye-sauye da za su hana mallakar bindiga.