Dole a hukunta Pistorius - Barry Steenkamp

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Barry yana tunanin 'yar sa ba dare ba rana

Barry Steenkamp, mahaifin budurwar dan tseren kasar Afrika ta Kudu Oscar Pistorius, ya ce dole ne a hukunta dan tseren kan kisan da ya yi wa 'yarsa.

Barry ya yi wadannan kalaman ne a yayin da yake bayanin lokacin da matarsa ta kira shi a wayar tarho ta shaida masa cewar an kashe 'yarsu, Reeva Steenkamp.

Barry dai ya yi ta kuka a lokacin da yake bayanin yadda yake sokawa kanshi allurar da yake yi wa kanshi ta masu fama da ciwon suga ko zai ji irin ciwon da 'yarsa ta ji a daren da ta mutu.

Mista Steenkamp ya kuma bukaci kotu ta nuna raunukan da suka yi sanadin mutuwar 'yarsa.

Ya kara da cewa, duk da dai matarsa ta ce ta yafe wa Oscar Pistorius a kan laifin da ya aikata, ya nanatawa kotu cewa dole a hukunta shi.

Barry ya kuma ce zai shirya domin ganawa da Oscar nan gaba.