Ko kun san illar teɓa a jikin ɗan adam?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Mutane dai suna ɗaukar teɓa a matsayin alamun ƙoshi

Wani sabon rahoto ya yi gargaɗin cewa ƙamarin da matsalar teɓa take ƙara yi a duniya na haifar da cutar yunwa.

Bisa al'ada dai an fi alaƙanta cutar yunwa da rashin abinci.

Amma rahoton ya gano cewa ba haka lamarin yake ba.

A cewar rahoton matsalar teɓa, wadda miliyoyin mutane ke fama da ita ce take janyowa mutanen ke zama da yunwa.

Jinin masu teɓar dai na ɗauke da tarin gishiri da sukari da maiƙo sannan kuma babu isassun abubuwa masu gina jiki.

Rahoton ya kuma yi gargaɗin cewa hakan ka iya haifar da babbar matsala ga harkar lafiya a duniya.

Sai dai rahoton ya ce idan har duniya ta miƙe tsaye wajen kawo ƙarshen matsalar ta teɓa za a samu waraka.