An kama mai 'safarar' mata a Tanzania

Tanzania Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption 'Yan Afrika da dama ne ke fita kasashen waje domin neman aiki

Jami'an shige da fice a Tanzania sun kama wani mutum da ake zargi da safarar mata zuwa kasashen nahiyar Asiya da kuma yankin Gabas ta Tsakiya.

Mutumin, wanda dan kasar Saudiyya ne, an kama shi ne tare da 'yan mata 12 daga kasar Burundi a birnin Dar es Salaam.

Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da gwamnati ta fitar cewa 'yan kasar 500 da suka fita waje domin yin aiki na korafin ana cin zarafinsu.

Wakilin BBC John Solombi a birnin Dar es Salaam, ya ce an yi wa 'yan matan alkawarin samun aikin yi amma hakan bai samu ba.

Ya kara da cewa da yawa daga cikinsu sun buge da yin karuwanci ko kuma aikatau.

Irin wannan matsala ba kasar Tanzania kawai ta shafa ba, domin kuwa kasashen Afrika da dama na fama da ita.