Olympics: Babu hadarin kamuwa da Zika a Brazil

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani taron gaggawa da kwamitin Hukumar lafiya ya yi, ya bayyana cewa babu hadari sosai game da yaduwar cutar Zika a lokacin gasar wasanni motsa jika na duniya da za a yi a kasar Brazil.

An dai yi ta kirayen-kirayen cewa ya kamata a jinkirta yin gasar, ko kuma fasa yi ma baki daya daga kasar.

Hukumar lafiyar ta jaddada matsayin da ta dauka tun da farko cewa bai kamata a yi kudin-goro ba wajen takaita tafiye-tafiye ko kasuwanci a kasashen da ke fama da annobar Zikar ba.

Dr Bruce Aylward babban Darakta ne a hukumar lafiya ta duniyar ya ce kwamitin ya yi ittifakin cewa hadarin yaduwar cutar Zika a lokacin gasar wasannin motsa jiki na duniya kadan ne, kuma lamarin zai kara sauki a lokacin hunturu, wato lokacin da za a yi gasar.

Sannan hukumomi a Brazil din na daukar matakan yaki da cutar.