Brazil: Ana zargin Michel Temer da cin hanci

Hakkin mallakar hoto getty

A Brazil, wata mummunar badakalar cin hancin da aka yi a kamfanin man kasar wato Petrobras ta shafi shugaban kasar na riko, Michel Temer.

Tsohon shugaban kamfanin man, Sergio Machado ne ya yi wannan zargin, lokacin da yake bayani ga masu shigar da kara.

Ya ce Michel Temer ya taba neman gudummuwar kudi daga cuwa-cuwar da ake yi don tallafa wa wani mutuminsa da ya tsaya takarar mukamin magajin-garin Sao Paulo, a shekarar 2012.

Sai dai shugaban kasar na riko ya musanta zargin.

A watan jiya ne dai Michel Temer ya karbi ragamar mulkin kasar, bayan jam'iyyarsa ta yi uwa da makarbiya wajen ganin an dakatar da shugabar kasar wato Dilma Russeff daga mukaminta domin ta fuskanci shara'a.