BH: Nijar na neman tallafin Faransa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban ya yi kiran ne bayan ya yi wata ganawa da takwaransa, Francois Hollande, a birnin Paris.

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya kara neman taimakon kasar Faransa a yunkurin da suke yi na murkushe kungiyar Boko Haram.

Ya kara da cewa akwai bukatar kawar da kungiyar saboda mutanen da ta kora daga gidajensu su samu damar komawa.

Kungiyar ta Boko Haram dai tana yawan kai hare-hare a Nijar musamman a garin Bosso da ke kan iyaka da Najeriya.

Ko a makon jiya sai da 'yan kungiyar suka kashe sojin Nijar 26 a garin na Bosso.

Faransa dai ta jibge dakarunta kimanin 3,500 a kasashe biyar na Afirka - Chadi, Mauritania, Niger, Mali da Burkina Faso - a yunkurin ta na fatattakar masu kaifin kishin Islama.