Nigeria: Za a ciyar da dalibai miliyan biyar

Makarantar firamare Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Najeriya na sa ran ciyar da dalibai miliyan 20 a shekaru hudu

Gwamnatin Najeriya ta ce ta ware Naira biliyan 93 a kasafin kudin 2016 domin ciyar da daliban firamare miliyan 5.5 "ingantaccen" abinci sau daya a kowacce rana.

Aikin ciyarwar, wanda za a shafe kwanaki 200 na karatu ana yi a matakin farko, na cikin ayyukan da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi alkawarin gudanarwa.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Laolu Akande ya ce za a ciyar da daliban ne da abincin da ake nomawa a cikin gida a wani yunkuri na bunkasa harkar noma da samar da ayyukan yi.

Mista Akande ya kara da cewa za a ninka yawan yaran da za a ciyar zuwa miliyan 20 nan da karshen wa'adin mulkin gwamnatin ta Buhari na shekara hudu.

Wannan shiri dai za a yi shi ne da hadin gwiwar gwamantin jihohi, sai dai Mista Akande ya ce, ''Ba a bukatar wani bangare na kudi daga wajensu a matakin farkon.''

Masu sharhi na nuna shakku kan irin tasirin da wannan shiri ka iya yi, ganin yawan daliban da kasar ke da su da kuma halin karancin kudin da gwamnatin kasar ke fama da shi

'Karin haske'

  • An kiyasta cewa za a kashe naira 70 ne kan abincin duk dalibi daya a kowacce rana.
  • Gwamnatin tarayya ce za ta dinga biyan masu dafa abincin kai tsaye daga aljihunta.
  • Ana tsammanin shirin zai bunkasa harkar noma da kuma samar da ayyukan yi.
  • Kazalika, zai taimaka wajen inganta lafiyar yara da kara musu karsashi wajen karatunsu.