Nigeria: Rikicin PDP ya fara shafar abokan hamayya

Hakkin mallakar hoto Sunusi Musa

A Nigeria bisa ga dukkan alamu rikicin jam'iyyar adawa ta PDP na kara girma, yayin da jam'iyyar ta soma zargin jam'iyyar APC mai mulki da hannu a cikin rikicin.

Tuni dai APC ta musanta zargin.

Cikin wannan makon ne dai Sanata Ali Modu Shariff da magoya bayansa suka karbi iko da hedikwatar jam'iyyar.

Bangaren Sanata Ahmed Makarfi ma ya dage cewa, shi ne halaltaccen shugaban jam'iyyar.

Tun bayan da ta sha kayi, jam'iyyar PDP ke fuskantar rikici iri-iri.

A cewar kakakin kwamitin riko na jam'iyyar wanda sanata Ahmad Muhammad Makarfi ke shugabanta, Prince Dayo Adeyeye, ya ce suna da wasu sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa sanata Ali Modu Shariff ya yi wata ganawa da wani gwamnan jam'iyyar APC a ranar lahadi inda suka cimma matsayar cewa za a bashi kowanne irin tsaro da kuma kudi domin ya kara rura wutar rikici a jam'iyyar.

Prince Dayo ya cigaba da cewa, bisa la'akari da yadda Ali Modu Shariff ya samu kariyar jami'an tsaro wajen kwace iko da Hedikwatar jam'iyyar, ya kara tabbatar musu da abinda suke zargi.

A nasa bangaren,sanata Ahmed Makarfi ya ce riga fada ba shi ne ganin sarki ba, domin har yanzu shi ke gudanar da jam'iyyar.