Ana tuhumar tsohon shugaban Guatemala

Ana zargin su da karbar miliyoyin daloli suka sokewa a mararsu Hakkin mallakar hoto JOHAN ORDONEZ AFP Getty Images

A kasar Guatemala, ana tuhumar tsohon shugaban kasar, Otto Perez Molina da mataimakiyarsa da laifin cin hanci da kuma halalta kudin haram, a cikin wani shirin da aka ce sun yi ta yashe kudin gwamnati suna sokewa a mararsu.

Ana dai zargin Otto Perez Molina da mataimakiyarsa, Roxana Baldetti da kuma wasu mutum 70 da karbar miliyoyin daloli, kuma sun yi amfani da kudin ne wajen sayen gidaje da motoci irin na kece-raini, sannan suka yi facakarsu da ragowar kudin wajen sayi-banza-sayi-wofi.

Ana dai zargin cewa sun samu kudin ne ta hanyar kashe-mu-raba a harkar ba da kwangilar ayyukan gwamnati, amma baki dayansu sun musanta wannan zargin.

Tuni dai tsofaffin shugabannin ke dakon shara'ar wasu batutuwan daban da suka tilasta musu yin murabus daga mukamansu.