Mai taya IS kutsen intanet zai sha dauri

Wani mutumin da ya taimaka wa kungiyar da jerin sunayen Sojojin Amurka mai suna Ardit Ferizi na fuskantar daurin shekara 25 a gidan yari.

Mutumin wanda dan asalin kasar Kosovo ne ya amince da aikata laifukan da aka tuhume shi, wadanda suka shafi taimaka wa abokan gabar Amurka.

Kotun dai ta yi zama ne a jihar Virginia, kuma akan yi daurin da yake kaiwa shekara 20 ga duk wanda aka kama da aikata irin wannan laifin.

Sai dai kuma zai iya fuskantar karin tuhama ta yin kutse ga bayanan sirrin ma'aikatar tarayya, tare satar bayanai, laifin da ake masa dairin shekara 5.

Ministan shara'ar Amurka, Dana Boente, a cikin wata sanarwa ya ce Ardit Ferizi ya jefa rayuwar Amurkawa sama 1000 cikin hadari.

Yanzu dai Ardit Ferizi na da shekara 21 da haihuwa, kuma ya danka wa kungiyar IS jerin sunayen Sojojin, alhali ya san hakan za ta ba mayakan kungiyar damar kai hari a kan daidaikun sojojin.

Cikin jerin sunayen da ya tura har da adireshin email da na gidaje da kuma lambobin wayar Sojojin Amurka 1,351.

Ardit Ferizi ya shaida wa kotun cewa ya mika jerin sunayen ne ga hannun Junaid Hussain, wani dan Burtaniya da ke yi kungiyar IS aiki, wanda aka kashe a watan Agustan da ya wuce lokacin da aka kai wani hari ta sama.

Matashin dai ya ce shi ma bai san dalilin da ya sanya shi aikata hakan ba.