Gwamnatin Jigawa na binciken Sule Lamido

Hakkin mallakar hoto google maps

'Yan hamayya a jihar Jigawa dake arewacin Nigeria sun mayar da martani a kan zargin da gwamatin jihar ta APC ta yi cewa an wawure wasu biliyoyin Nairori daga kananan hukumomin jihar a zamanin gwamnatin da ta wuce.

Gwamnatin ta APC dai tace tuni ta kaddamar da bincike kan almundahanar da aka tafka a lokacin gwamnatin PDP da ta gabata.

Wannan ne dai karon farko da gwamnatin ta Jigawa ta bayyana cewa ta na gudanar da bincike a kan zargin almundahana da kudaden jihar.

Gwamnan jihar, Alhaji Badaru Abubakar, ya ce a yanzu za su fara ne da kananan hukumomi kafin su kai ga matakin jiha.

Sai dai kuma, wasu jami'an tsohuwar gwamnatin da ta shuden sun mayar da martani inda suka ce basa tsoron duk wani bincike, domin ciki da gaskiya wuka bata huda shi.