Nigeria: 'Yan majalisa sun 'ɓige da neman karuwai'

Majalisar Dokokin Nigeria

Asalin hoton, national assembly

Bayanan hoto,

'Yan majalisar sun ce zargin ba shi da tushe ko makama

Gwamnatin Amurka ta zargi wasu 'yan majalisar wakilan Najeriya da neman karuwai a lokacin da suka kai wata ziyarar aiki kasar kwanakin baya.

Wata wasika da jakadan Amurka a Najeriya, Mr. James Entwistle, ya aikewa shugaban majaliasar wakilan, Yakubu Dogara, ya zargi 'yan majalisa uku daga cikin goma da suka kai ziyara kasar da nuna rashin kamala da yunkurin yin fyade da neman karuwai.

A cewar Mr Entwistle 'yan majalisar su ne: Mohammed Garba Gololo (APC, Bauchi), Samuel Ikon (PDP, Akwa Ibom) da kuma Mark Gbillah (APC, Benue).

Sai dai 'yan majalisar sun yi watsi da wadannan zarge-zarge, suna cewa ba su da tushe ballantana makama, tare da yin barazanar kai Mr Entwistle kotu.

Ya kara da cewa Mohammed Garba Gololo ya yi yunkurin rungumar wata ma'aikaciya da ta je gyara masa dakinsa da zummar yin lalata da ita.

A martanin da ya mayarwa jakadan na Amurka Mohammed Garba Gololo: "Wadannan zarge-zarge ba su da kanshin gaskiya. Ban rungumi wata ma'aikaciyar otal ba, ballantana na bukaci yin lalata da ita."

A cewar sa, "Ina so Amurka ta janye wannan labari sannan ta nemi afuwa ta idan ba haka ba zan sa lauyoyi na su shigar da kara kan cin zarafi da ɓata suna na da ake son yi."

Mr. Entwistle ya kara da cewa "Mark Terseer Gbillah da Samuel Ikon sun bukaci ma'aikatan wurin ajiye motoci na otal din da su nemo musu karuwai."

Sai dai mai magana da yawun shugaban majalaisar wakilan, Turaki Hassan, ya shaida wa BBC cewa su ma ragowar mutane biyu da aka zarga sun musanta kalaman na Amurka.

"Majalisa ta mika takardan koken, kuma dukkansu sun mayar da martani a rubuce, inda suka musanta aikata abin da aka zarge su da shi.

Wani jami'i a ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, ya shaida wa BBC cewa ba za su yi magana kan abubuwan diflomasiyya da suka shafi daidaikun mutane ba.