'Ku yi taka-tsan-tsan da manhajar IS'

Hakkin mallakar hoto Lai Mohammed Facebook
Image caption Sanarwar ta fito ne daga ofishin ministan yada labarai na Najeriya, Lai Muhammad

Gwamnatin Najeriya ta ja hankalin 'yan kasar game da wata manhaja ta wayar salula da kungiyar ISIS ke amfani da ita wajen jan hankalin yara domin sauya masu akida.

Ita dai wannan sabuwar manhaja da kungiyar ta ISIS ta kadamar tana amfani da ita ne a Iraki da Syria domin cusa ra'ayin jahadi ga yara.

A cikin wata sanarwa daga ofishin ministan watsa labarai da al'adu na Najeriya, Lai Muhammad, ta sanar da cewa manhajar mai suna ''Huroof'' na dauke da haruffan larabci ne.

Ta kuma ce kungiyar ta ISIS na amfani da ita wajen koyar da yara harufan larabci da koyar da su yadda ake harba bindiga da amfani da tankokin yaki da yadda ake harba rokoki.

Ita dai wannan manhaja na amfani da launi da dama da ke jan hankalin yara ta yadda za su dukufa su mayar da hankalinsu kacokam kan lamarin.

Image caption Manhajar na da kaloli na jan hankalin yara

''Don haka ana kira ga al'umma musamman uwayen yara da su yi taka-tsan-tsan su kuma sa ido don ka da 'ya'yansu, su tsunduna cikin wannan yanayi na sauya akida ta wannan hanya da ISIS ke amfani da ita,'' in ji sanarwar.

Masu sharhi kan lamarin tsaro sun bayyana cewa rashin sa ido kan yara game da irin abubuwan da suke yi na da illa matuka, wanda hakan kan iya jawo wani babban bala'i a cikin al'umma da ma kasa baki daya.